36 sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama'arka Isra'ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama'arka gādo.
37 “Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama'arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu,
38 sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Idan ɗaya daga cikin jama'arka Isra'ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'a wajen wannan Haikali,
39 sai ka ji addu'arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,
40 domin mutanenka su yi tsoronka a dukan kwanakinsu a ƙasar da ka ba kakanninmu.
41 “Sa'ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka,
42 da manyan al'amura da ka yi wa jama'arka, ya zo domin ya yi maka sujada, da kuma addu'a gare ka a wannan Haikali,