12 Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra'ila, kada ka yi halin dabba.
13 Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra'ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”
14 Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.
15 Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”
16 Sai ta ce masa, “A'a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.”Amma bai kasa kunne gare ta ba.
17 Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”
18 Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.