28 Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”
29 Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.
30 Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa'ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka.
31 Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.”Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”
32 Da Dawuda ya hau kan dutse inda ake yi wa Allah sujada, sai ga amininsa Hushai Ba'arkite, da ketacciyar riga, da ƙura a kansa, ya zo ya taryi Dawuda.
33 Dawuda kuwa ya ce masa, “Idan ka tafi tare da ni za ka zama mini nawaya.
34 Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, ‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.’ Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.