1 Dawuda kuwa ya shirya sojojin da suke tare da shi, sa'an nan ya naɗa musu shugabanni na dubu dubu da na ɗari ɗari.
2 Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa'an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”
3 Amma sojojin suka ce, “Ba za ka tafi tare da mu ba, gama idan muka gudu, ba za su kula da mu ba. Ko rabinmu sun mutu, ba za su kula ba, gama kai kana bakin mutum dubu goma (10,000) na mutanenmu. Zai fi kyau kuma ka zauna cikin gari ka riƙa aika mana da taimako.”
4 Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.