28 Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra'ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.
29 Abner da mutanensa suka bi dare farai, suka ratsa Araba, suka haye Urdun. Suka yi ta tafiya dukan safiyan nan, suka shige Bitron, har suka kai Mahanayim.
30 Da Yowab ya komo daga runtumar Abner, ya tattara mutanensa duka, sai ya ga an rasa mutum goma sha tara daga cikin mutanen Dawuda, banda Asahel.
31 Amma barorin Dawuda suka kashe mutanen Biliyaminu mutum ɗari uku da sittin daga cikin waɗanda suke tare da Abner.
32 Suka ɗauki Asahel, suka tafi suka binne shi a kabarin mahaifinsa a Baitalami. Yowab kuwa da mutanensa suka bi dare farai, gari ya waye musu a Hebron.