12 Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya.
13 Sa'ad da aka kawar da ita daga kan hanya, dukan mutane kuwa suka bi Yowab domin su bi sawun Sheba ɗan Bikri.
14 Sai Sheba ya bibiya kabilan Isra'ila, har ya kai Abel-bet-ma'aka. Dukan dangin Beri kuwa suka taru suka bi shi zuwa cikin garin.
15 Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma'aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun.
16 Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.”
17 Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?”Ya ce, “I, ni ne.”Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.”Ya ce, “Ina sauraronki.”
18 Ta ce, “A dā sukan ce, ‘A nemi shawara a Abel,’ gama a can ake raba gardama.