14 Sai Sheba ya bibiya kabilan Isra'ila, har ya kai Abel-bet-ma'aka. Dukan dangin Beri kuwa suka taru suka bi shi zuwa cikin garin.
15 Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma'aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun.
16 Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.”
17 Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?”Ya ce, “I, ni ne.”Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.”Ya ce, “Ina sauraronki.”
18 Ta ce, “A dā sukan ce, ‘A nemi shawara a Abel,’ gama a can ake raba gardama.
19 Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra'ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”
20 Yowab ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Ba zan lalatar ko in hallakar da birninku ba.