23 Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra'ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro.
24 Adoniram shi ne shugaban aikin gandu, Yehoshafat, ɗan Ahilud, shi ne marubuci.
25 Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci.
26 Aira mutumin Yayir shi ne mashawarcin Dawuda.