6 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
7 A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji,Na yi kira ga Allah domin taimako.Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata,Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.
8 “Sa'an nan duniya ta yi tangaɗi, ta girgiza,Harsashin sararin sama ya yi makyarkyata, ya raurawa, saboda fushin Allah.
9 Hayaƙi ya fito daga kafafen hancinsa,Harshen wuta mai cinyewa da garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
10 Ya jā sararin sama baya ya sauko,Da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
11 Ya hau kerub, ya tashi sama,Ya yi tafiya ta fikafikan iska.
12 Ya rufe kansa da duhu,Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,