10 shi kuwa ya tsaya, ya yi ta yaƙi da Filistiyawa, har hannunsa ya ƙage, har bai iya ɓanɓaruwa daga takobinsa ba. Ubangiji ya ba da babbar nasara a wannan rana. Bayan an gama sai Isra'ilawa suka koma wurin Ele'azara don su kwashi ganima kawai.
11 Biye da Ele'azara kuma, sai Shamma, ɗan Agi, daga Harod. Filistiyawa suka taru a Lihai, inda akwai wata gonar wake. Isra'ilawa kuwa suka guji wa Filistiyawa.
12 Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta. Ya kuma kashe Filistiyawa. Ubangiji ya ba da babbar nasara.
13 Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.
14 Dawuda yana cikin kagara, ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuwa tana a Baitalami.
15 Dawuda ya ji marmari, ya ce, “Kai, da ma wani zai ba ni ruwan rijiyar ƙofar garin Baitalami in sha!”
16 Shahararrun jarumawan nan uku kuwa suka sheƙa a guje, suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka tafi, suka ɗebo ruwa daga rijiyar ƙofar garin Baitalami, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda bai sha ba, ya zuba shi hadaya a gaban Ubangiji.