1 Sa'ad da sarki yake zaune a gidansa, Ubangiji kuma ya hutasshe shi daga fitinar abokan gābansa da suke kewaye da shi,
2 sai sarki ya ce wa annabi Natan, “Duba, ga shi, ina zaune a gidan katakon al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana a alfarwa.”
3 Natan kuwa ya ce wa sarki, “Sai ka yi abin da yake a zuciyarka, gama Ubangiji yana tare da kai.”
4 Amma a daren nan Ubangiji ya yi magana da Natan.
5 Ya ce, “Tafi, ka faɗa wa bawana Dawuda, ka ce, in ji Ubangiji, ‘Ɗakin zama za ka gina mini?
6 Har wa yau ban taɓa zama a ɗaki ba, tun lokacin da na fito da Isra'ilawa daga Masar, amma a alfarwa nake kai da kawowa daga wannan wuri zuwa wancan.
7 A cikin kai da kawowata tare da dukan jama'ar Isra'ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra'ila waɗanda na sa su lura da jama'ata Isra'ila, ya gina mini ɗaki na katakon al'ul ba.’