1 A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai.
2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, gama ya aikata irin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ilawa su yi zunubi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba.
3 Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel.
4 Sai Yehowahaz ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji shi, gama ya ga wahalar da Isra'ilawa suke ciki, wato yadda Sarkin Suriya yake musguna musu.