32 A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
33 Yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha, 'yar Zadok.
34 Yotam ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Azariya, ya yi.
35 Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.
36 Sauran ayyukan Yotam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
37 A kwanakin nan Ubangiji ya fara aiken Rezin Sarkin Suriya da Feka ɗan Remaliya su yi yaƙi da Yahuza.
38 Yotam ya rasu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.