1 A shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.
2 Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarautar, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Bai yi abin da yake da kyau a gaban Ubangiji Allahnsa ba, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.
3 Ya bi halin sarakunan Isra'ila. Har ma ya yi hadaya ta ƙonawa da ɗansa, kamar mugayen ayyukan al'ummai da Ubangiji ya kora a gaban mutanen Isra'ila.
4 Ya kuma miƙa hadaya da turaren ƙonawa a wuraren tsafi na kan tuddai da ƙarƙashin itatuwa masu duhuwa.
5 Rezin Sarkin Suriya kuwa, da Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, suka kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye Ahaz da yaƙi, amma ba su ci shi ba.
6 A lokacin nan kuma Sarkin Edom ya sāke ƙwace Elat, ya kori Yahudawa daga cikinta, Edomawa suka zo suka zauna a ciki har wa yau.
7 Ahaz kuwa ya aiki manzanni wurin Tiglat-filesar, mai mulkin Assuriya, ya ce, “Ni baranka ne, ɗanka kuma, ka zo ka cece ni daga hannun Sarkin Suriya da Sarkin Isra'ila, waɗanda suke yaƙi da ni.”