8 Ahaz kuma ya kwashe azurfa da zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, da wadda take cikin baitulmalin sarki, ya aika wa mai mulkin Assuriya kyauta.
9 Tiglat-filesar ya ji roƙonsa, sai ya zo ya faɗa wa Dimashƙu da yaƙi, ya ci ta. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa Kir. Ya kuma kashe sarki Rezin.
10 Sa'ad da sarki Ahaz ya tafi Dimashƙu don ya sadu da Tiglat-filesar, Sarkin Assuriya, ya ga bagaden da yake a Dimashƙu, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayaninsa.
11 Uriya firist kuwa, ya gina bagaden bisa ga yadda sarki Ahaz ya aika masa daga Dimashƙu. Uriya firist, ya gina bagaden kafin sarki Ahaz ya komo daga Dimashƙu.
12 Da sarki ya komo daga Dimashƙu, ya hango bagaden, sai ya tafi kusa da shi.
13 Sa'an nan ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayarsa ta gari, da hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta salama a bisa bagaden.
14 Sai ya kawar da bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi arewacin sabon bagadensa.