5 Sa'an nan Sarkin Assuriya ya kai wa dukan ƙasar yaƙi, har ya kai Samariya. Ya kewaye Samariya da yaƙi shekara uku.
6 A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.
7 Wannan abu ya sami Isra'ila saboda sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fito da su daga ƙasar Masar, daga hannun Fir'auna, Sarkin Masar. Suka bauta wa gumaka.
8 Suka bi al'adun al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora a gabansu, da al'adun da sarakunan Isra'ila suka kawo.
9 Jama'ar Isra'ila kuma suka yi wa Ubangiji Allahnsu abubuwan da ba daidai ba, daga ɓoye. Sun gina wa kansu matsafai a dukan garuruwansu daga hasumiya zuwa birni mai garu.
10 Suka kuma kafa wa kansu ginshiƙai da siffofin gumakan Ashtarot a kowane tudu da a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.
11 Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.