19 Sa'an nan Rabshake ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya, cewa mai girma, Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ga wa kake dogara?
20 Kana tsammani maganganu kurum su ne dabara da ƙarfin yin yaƙi? To, ga wa ka dogara har da ka tayar mini?
21 Ga shi yanzu, kana dogara ga Masar, wannan karyayyen sandan kyauro, wanda yakan yi wa hannun mutumin da yake tokarawa da shi sartse. Haka Fir'auna Sarkin Masar, yake ga dukan waɗanda suke dogara gare shi.’
22 “Amma idan ka ce mini, ‘Ina dogara ga Ubangiji Allahnmu,’ to, ba masujadansa na kan tuddai da bagadansa ne Hezekiya ya rurrushe ba? Yana ce wa mutanen Yahuza da Urushalima, ‘Za ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima?’
23 Sai ka zo, ku daidaita da ubangidana, Sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu (2,000), idan za ka iya samun mahayansu.
24 Ba ka isa ka kara da ko mafi ƙanƙanta na shugabannin sojojin maigidana ba, amma har kana dogara ga Masar don samun karusai da mahaya?
25 Kana tsammani, ba da yardar Ubangiji ba ne na kawo wa wurin nan yaƙi don a hallaka shi? Gama Ubangiji ya ce mini, ‘Ka kai wa wannan ƙasa yaƙi don ka hallaka ta.’ ”