23 Sai ka zo, ku daidaita da ubangidana, Sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu (2,000), idan za ka iya samun mahayansu.
24 Ba ka isa ka kara da ko mafi ƙanƙanta na shugabannin sojojin maigidana ba, amma har kana dogara ga Masar don samun karusai da mahaya?
25 Kana tsammani, ba da yardar Ubangiji ba ne na kawo wa wurin nan yaƙi don a hallaka shi? Gama Ubangiji ya ce mini, ‘Ka kai wa wannan ƙasa yaƙi don ka hallaka ta.’ ”
26 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa, suka ce wa Rabshake, “Muna roƙonka, ka yi magana da mu barorinka da harshen Aramiya gama muna jinsa, kada ka yi magana da mu da harshen Yahudanci, har mutanen da suke kan garu su ji.”
27 Amma Rabshake ya ce musu, “Ai, ubangidana bai aike ni in yi wannan magana ga ubangidanku da ku kaɗai ba, amma ga dukan mutanen da suke zaune a kan garu, waɗanda aka ƙaddara su tare da ku don su ci najasarsu su sha fitsarinsu.”
28 Sa'an nan Rabshake ya tsaya, ya yi kira da ƙarfi da harshen Yahudanci, ya ce, “Ku ji maganar mai girma, Sarkin Assuriya!
29 Sarki ya ce, ‘Kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, gama ba zai iya cetonku daga hannuna ba.