5 Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?”Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
6 Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.”Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.
7 Waɗansu annabawa hamsin kuma suka tafi tare da su. Iliya da Elisha suka tsaya kusa da kogi, annabawa hamsin ɗin suka tsaya da ɗan nisa.
8 Sa'an nan Iliya ya tuɓe alkyabbarsa, ya naɗe ta, ya bugi ruwa da ita, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, dukansu biyu fa suka taka sandararriyar ƙasa suka haye.
9 Sa'ad da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka faɗa mini abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga wurinka.”Elisha ya ce, “Bari in sami rabo daga cikin ikonka domin in gaje ka.”
10 Iliya kuwa ya ce, “Ka roƙi abu mai wuya, duk da haka, idan ka gan ni lokacin da za a ɗauke ni, to, abin da ka roƙa za ka samu, amma idan ba ka gan ni ba, to, ba za ka samu ba ke nan.”
11 Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa.