27 Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama'ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama'ar Isra'ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”
28 Sauran ayyukan Yosiya da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
29 A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.
30 Fādawansa kuwa suka ɗauko gawarsa a karusa daga Magiddo, suka kawo Urushalima, suka binne a kabarinsa.Sai jama'ar ƙasa suka naɗa Yehowahaz ɗan Yosiya sarki a matsayin tsohonsa.
31 Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Hamutal 'yar Irmiya na Libna.
32 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi.
33 Fir'auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya.