5 Ya kuma tuɓe firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuza suka naɗa domin su ƙona turare a matsafai na kan tuddai a garuruwan Yahuza, da kewayen Urushalima, da firistoci waɗanda suka ƙona turare ga Ba'al, da rana, da wata, da taurari, da dukan rundunan sama.
6 Sai sarki ya fitar da gunkiyan nan Ashtoret, daga cikin Haikalin Ubangiji a Urushalima, ya kai Kidron, ya ƙone ta a ƙoramar Kidron, ta zama toka, ya kuwa watsar da tokar a makabarta.
7 Ya rurrushe ɗakunan karuwai mata da maza da suke a Haikalin Ubangiji, wato wurin da mata suke saƙa labulan gunkiyar.
8 Ya fitar da dukan firistoci daga cikin garuruwan Yahuza, sa'an nan ya lalatar da matsafai na kan tuddai inda firistoci suka ƙona turare, tun daga Geba har zuwa Biyer-sheba. Ya kuma rurrushe matsafai na kan tuddai waɗanda suke a ƙofofin shiga ƙofar Joshuwa, hakimin birnin, waɗanda suke hagu da ƙofar birnin.
9 Duk da haka firistoci matsafai na kan tuddai ba su haura zuwa bagaden Ubangiji a Urushalima ba, amma suka ci abinci marar yisti tare da 'yan'uwansu.
10 Ya kuma lalatar da Tofet, wurin da yake kwarin 'ya'yan Hinnom, don kada kowa ya ƙara miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya ta ƙonawa ga Molek.
11 Ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuza suka keɓe wa rana, a ƙofar Haikalin Ubangiji, kusa da shirayin Natan-melek shugaban shirayin da yake cikin farfajiya. Haka kuma ya ƙone karusai waɗanda aka yi wa rana.