1 Amma Elisha ya ce, “Kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce! Gobe war haka za a sayar da mudu na lallausan gari a bakin shekel guda, da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel guda a ƙofar garin Samariya.”
2 Amma dogarin da yake tare da sarki ya ce wa Elisha, “Ko da Ubangiji kansa zai buɗe tagogin sama, wannan abu ba zai yiwu ba.”Elisha kuwa ya ce, “Za ka gani da idanunka, zai faru, amma ba za ka ci ba.”
3 Akwai mutum huɗu, kutare, waɗanda suke zaune a bakin ƙofar gari, sai suka ce wa junansu, “Me ya sa muke zaune nan har mu mutu?
4 Idan mun ce, ‘Bari mu shiga birni,’ yunwa tana birnin, za mu mutu a wurin. Idan kuma mun zauna a nan za mu mutu. Saboda haka bari mu tafi sansanin Suriyawa, idan sun bar mu da rai, za mu rayu, idan kuwa sun kashe mu, za mu mutu.”