1 Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”
2 Sai matar ta tashi, ta yi kamar yadda annabi Elisha ya faɗa mata. Ta tafi, ita da iyalinta suka zauna a ƙasar Filistiyawa har shekara bakwai.
3 A ƙarshen shekara bakwai ɗin, matar ta komo daga ƙasar Filistiyawa, ta tafi wurin sarki, ta roƙe shi a mayar mata da gidanta da gonarta.
4 A lokacin kuwa sarki yana tare da Gehazi, wato baran annabi Elisha, ya ce, “Ka faɗa mini dukan mu'ujizan da Elisha ya yi.”