1 Da mulkin Rehobowam ya kahu, ya kuma yi ƙarfi, sai Rehobowam da dukan Isra'ilawa tare da shi suka bar bin shari'ar Ubangiji.
2 A shekara ta biyar ta mulkin sarki Rehobowam, Isra'ilawa ba su bi Ubangiji da aminci ba, saboda haka Shishak, Sarkin Masar, ya hauro don ya yi yaƙi da Urushalima.
3 Aka faɗo masa da karusai dubu da ɗari biyu (1,200), da mahayan dawakai mutum dubu sittin (60,000). Mutanen da suka taho tare da sarki Shishak daga Masar, ba a san adadinsu ba, akwai Libiyawa, da Sukkimiyawa, da kuma Habashawa.
4 Ya ci birane masu kagara na Yahuza, har ya dangana da Urushalima.
5 Sai annabi Shemaiya ya zo wurin Rehobowam da sarakunan Yahuza waɗanda suka tattaru a Urushalima saboda Shishak, ya ce musu, “Ubangiji ya ce kun yashe shi, don haka shi ma ya bashe ku a hannun Shishak.”
6 Sai sarakunan Isra'ila tare da sarki Rehobowam, suka ƙasƙantar da kansu, suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”