17 A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.
18 Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da yake ciki.
19 Dukan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar a zamaninsa, sa'ad da ya zama marar aminci, mun shirya su mun tsarkake su, suna nan a gaban bagaden Ubangiji.”
20 Sarki Hezekiya kuwa ya tashi da sassafe ya tattara manyan gari suka haura zuwa Haikalin Ubangiji.
21 Suka kawo bijimai bakwai, da raguna bakwai, da 'yan raguna bakwai, da bunsurai bakwai, domin yin hadaya don zunubi saboda mulkin, da Wuri Mai Tsarki, da kuma Yahuza. Sai ya umarci firistoci, wato 'ya'yan Haruna, maza, su miƙa su a kan bagaden Ubangiji.
22 Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin, suka yayyafa a jikin bagaden. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka nan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.
23 Sa'an nan suka kawo wa sarki da taron jama'a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran.