25 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin jama'arka Isra'ila, ka komo da su ƙasar da ka ba su, su da kakanninsu.
26 “Sa'ad da aka kulle sammai, ba ruwan sama saboda sun yi maka zunubi, sa'an nan suka fuskanci wurin nan suka yi addu'a, suka shaida sunanka, suka juyo suka daina zunubinsu a sa'ad da ka hukunta su,
27 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin bayinka, wato jama'arka Isra'ila, lokacin da ka koya musu kyakkyawar hanya da za su bi. Sai ka sa a yi ruwa a ƙasarka, wadda ka ba jama'arka gādo.
28 “Idan ana yunwa a ƙasar, ko annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fārā, ko gamzari, ko da maƙiyansu za su kewaye biranensu da yaƙi, ko kowace irin annoba, da kowace irin cuta da take akwai,
29 kowace irin addu'a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama'ar Isra'ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali,
30 sa'an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al'amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,
31 don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.