31 don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.
32 “Haka kuma baƙo wanda ba cikin jama'arka Isra'ila yake ba, idan ya taho daga wata ƙasa mai nisa saboda girman sunanka da ƙarfin ikonka, in ya zo ya yi sujada, yana fuskantar Haikalin nan,
33 ka ji daga Sama wurin zamanka, ka kuwa aikata bisa ga dukan irin roƙon da baƙon ya yi gare ka. Domin ta haka sauran al'umman duniya za su san sunanka, su kuma yi tsoronka, yadda jama'arka Isra'ila suke yi, za su kuma sani cewa wannan Haikali da na gina, ana kiransa da sunanka.
34 “Sa'ad da jama'arka za su fita don yin yaƙi da magabtansu, duk dai ko ta ina ne za ka aike su, in sun yi addu'a gare ka, suna fuskantar wannan birni wanda kai ka zaɓa, da Haikalin nan da na gina saboda sunanka,
35 sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, ka biya muradinsu.
36 “Sa'ad da suka yi maka zunubi (gama ba wani ɗan adam da ba ya yin zunubi), ka kuwa yi fushi da su, har ka bashe su a hannun magabtansu, magabtansu suka kakkama su suka kai wata ƙasa ta nesa ko ta kusa,
37 duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, ‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,’