7 Na hana wa shuke-shukenku ruwaA lokacin da suka fi bukata.Na sa a yi ruwa a wani birni,A wani birni kuwa na hana,Wata gonar ta sami ruwan sama,Amma wadda ba ta samu ba tabushe.
8 Ƙishirwa ta sa jama'a su tafke harbirane biyu ko ukuSuka tafi neman ruwa a birnin dasuke maƙwabtaka da shi,A nan ma ba su sami isasshen ruwansha ba,Duk da haka ba ku komo wurinaba.
9 “Na sa darɓa, da domanaSu lalatar da amfanin gonakinku.Fāra kuma ta cinye lambunankuDa gonakin inabinku, da itatuwanɓaurenku,Da na zaitun ɗinku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.
10 “Na aukar muku da annoba irinwadda na aukar wa Masar.Na karkashe samarinku a wurinyaƙi,Na kwashe dawakanku.Na cika hancinku da ɗoyinsansaninku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.
11 “Na hallakar da waɗansunkuKamar yadda na hallakar da Sadumada Gwamrata.Kamar sanda kuke, wanda aka fizgedaga wuta.Duk da haka ba ku komo wurinaba.
12 Saboda haka, jama'ar Isra'ila,Ga abin da zan yi muku,Zan kuwa yi shi duk,Sai ku yi shirin zuwa gabanUbangiji.”