9 Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,Da a kan birane masu garu.
10 Kun ƙi wanda ya tsaya a kanadalci,Da mai faɗar ainihin gaskiya a gabanshari'a.
11 Kun matsa wa talakawa lamba,Kun ƙwace musu abincinsu.Saboda haka kyawawan gidajen nanda kun gina da dutse,Ba za ku zauna a cikinsu ba,Ba kuwa za ku sha ruwan inabinnanDaga kyawawan gonakin inabinkuba.
12 Na san irin zunuban da kuke yi,Da mugayen laifofin da kuka aikata.Kuna wulakanta mutanen kirki,Kuna cin hanci,Kuna hana a yi wa talakawa shari'aradalci a majalisa.
13 Ashe, ba abin mamaki ba ne,Da masu hankali suka kame bakinsuA waɗannan kwanaki na mugunta.
14 Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, bamugunta ba,Domin ku tsira.Sa'an nan ne Ubangiji AllahMaɗaukakiZai kasance tare da ku sosai,Kamar yadda kuka ɗauka!
15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunacinagarta,Ku yi adalci cikin majalisaralƙalanku!Watakila Ubangiji Allah MaiRundunaZai yi wa sauran da suka ragu nawannan al'umma alheri.