13 A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.
14 Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.
15 Da na dubi talikan, sai na ga ƙafafu huɗu kamar na keke a ƙasa kusa da talikan. Ɗaya domin kowane taliki.
16 Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa.
17 Sa'ad da suke tafiya, suna tafiya a kowane waje, ba sai sun juya ba.
18 Akwai waɗansu ƙarafa kamar zobe, da idanu kuma tantsai kewaye da ƙafafun.
19 Duk sa'ad da talikan suka motsa, sai kuma ƙafafun su motsa tare da su. Idan kuma talikan suka ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga tare da su.