25 Sai aka ji murya ta fito daga saman al'arshi ɗin.
26 A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta.
27 Daga kwankwasonsa zuwa sama yana walƙiya kamar tagullar da aka kewaye ta da wuta. Daga kwankwasonsa zuwa ƙasa yana haskakawa kamar wuta.
28 Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.