1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.
3 Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne.
4 Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi.
5 Ka huda katanga a kan idonsu, sa'an nan ka fita daga ciki.