12 Sarkin da yake cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa.
13 Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.
14 Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko'ina. Zan zare takobi in runtume su.
15 “Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe.
16 Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, da yunwa, da annoba, don su tuba, su hurta dukan ayyukansu na banƙyama a cikin al'ummai inda suka tafi. Za su sani ni ne Ubangiji.”
17 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
18 “Ɗan mutum, ka ci abincinka da rawar jiki, ka sha ruwanka da makyarkyata da damuwa.