20 Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
21 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
22 “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra'ila cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba”?
23 Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.
24 “Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra'ila.
25 Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”
26 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,