24 “Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra'ila.
25 Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”
26 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
27 “Ɗan mutum, ga shi, mutanen Isra'ila suna cewa, ‘Wahayin da ya gani na wani lokaci ne can gaba, yana annabci a kan wani zamani ne na can.’
28 Domin haka ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji na ce maganata ba za ta yi jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”