9 “Ɗan mutum, ashe, mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan, ko suka ce maka, ‘Me kake yi?’
10 Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra'ila, waɗanda suke cikinta.’
11 Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.’
12 Sarkin da yake cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa.
13 Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.
14 Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko'ina. Zan zare takobi in runtume su.
15 “Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na watsa su cikin sauran al'umma da cikin ƙasashe.