28 “Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa domin ba ki ƙoshi ba. Kin yi karuwanci da su duk da haka ba ki ƙoshi ba.
29 Kin yawaita karuwancinki da Kaldiya, ƙasar ciniki, duk da haka ba ki ƙoshi ba.
30 “Kin cika uzuri,” in ji Ubangiji Allah. “Duba, kin aikata waɗannan abubuwa duka, ayyuka na karuwa marar kunya.
31 Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.
32 Ke mazinaciyar mace, mai kwana da kwartaye maimakon mijinki!
33 Maza sukan ba dukan karuwai kuɗi, amma ke ce mai ba kwartayenki kuɗi, kina ba su kuɗi don su zo wurinki don kwartanci daga ko'ina.
34 Kin yi dabam da sauran mata a cikin karuwancinki, da yake ba wanda ya bi ki don yin karuwanci, ba a ba ki kuɗi, ke ce kike ba da kuɗi, domin haka kin sha bamban.”