58 Kina ɗauke da hukuncin lalatarki da na abubuwanki masu banƙyama, ni Ubangiji na faɗa.”
59 “Ni Ubangiji Allah na ce, zan yi miki yadda kika yi, ke da kika yi rantsuwar kafara, kika ta da alkawari.
60 Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin kuruciyarki. Zan ƙulla madawwamin alkawari da ke.
61 Sa'an nan za ki tuna da ayyukanki, ki ji kunya, sa'ad da na ɗauki yarki da ƙanwarki, na ba ki su, su zama 'ya'yanki mata, amma ba a kan alkawarin da na yi da ke ba.
62 Zan ƙulla alkawarina da ke, za ki sani ni ne Ubangiji,
63 domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa'ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”