1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa,‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami,Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu’?
3 “Ni Ubangiji Allah na ce, hakika, ba za a ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba.
4 Ga shi, dukan rayuka nawa ne, da ran uban da na ɗan, duka nawa ne. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu.
5 “Ga irin mutumin da zai rayu, mutumin da yake adali, yana bin shari'a, yana kuma aikata abin da yake daidai,
6 idan ba ya cin abinci a ɗakin tsafi, bai bauta wa gumakan mutanen Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, ba yakan kwana da mace a lokacin hailarta ba,
7 wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa,