10 “Amma idan ya haifi ɗa wanda ya zama ɗan fashi, mai kisankai, yana yi wa ɗan'uwansa ɗaya daga cikin abubuwan nan, [ko shi kansa,
11 bai yi irin waɗannan abubuwa ba,] wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa,
12 yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,
13 yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.
14 “Amma idan wannan mutum ya haifi ɗa wanda ya ga dukan laifofin da mahaifinsa ya yi, sa'an nan ya ji tsoro, bai kuwa yi haka ba,
15 bai ci abinci a ɗakin tsafi ba, bai bauta wa gumakan mutanen gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba,
16 bai ci zalin kowa ba, bai karɓi jingina ba, bai yi ƙwace ba, amma yana ba mayunwaci abinci, yana ba huntu tufa,