10 “ ‘Mahaifiyarka tana kama da kurangar inabi,Wadda aka dasa kusa da ruwa,Ta ba da 'ya'ya da rassa da yawa, saboda isasshen ruwa.
11 Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki,Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan,Ana hangenta daga nesa.
12 Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi,Aka jefar da ita ƙasa.Iskar gabas ta busar da ita,'Ya'yanta suka kakkaɓe,Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.
13 Yanzu na dasa ta a jeji, cikin busasshiyar ƙasa,
14 Wuta ta fito daga jikintaTa cinye rassanta da 'ya'yanta,Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki.Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.’ ”