3 Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,Ya zama sagari,Sai ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.
4 Da al'ummai suka ji labarinsa,Sai suka kama shi cikin wushefensu,Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa Masar.
5 Sa'ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi,Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta,Ta goye shi ya zama sagari.
6 Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki,Ya zama sagari,Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.
7 Ya lalatar da kagaransu,Ya mai da biranensu kufai,Ƙasar da waɗanda suke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.
8 Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje,Sun kafa masa tarko,Suka kama shi cikin wushefensu.
9 Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka sa shi cikin suru,Suka kai shi wurin Sarkin Babila.Suka sa shi a kurkuku don kada a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra'ila.’ ”