6 Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki,Ya zama sagari,Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.
7 Ya lalatar da kagaransu,Ya mai da biranensu kufai,Ƙasar da waɗanda suke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.
8 Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje,Sun kafa masa tarko,Suka kama shi cikin wushefensu.
9 Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka sa shi cikin suru,Suka kai shi wurin Sarkin Babila.Suka sa shi a kurkuku don kada a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra'ila.’ ”
10 “ ‘Mahaifiyarka tana kama da kurangar inabi,Wadda aka dasa kusa da ruwa,Ta ba da 'ya'ya da rassa da yawa, saboda isasshen ruwa.
11 Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki,Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan,Ana hangenta daga nesa.
12 Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi,Aka jefar da ita ƙasa.Iskar gabas ta busar da ita,'Ya'yanta suka kakkaɓe,Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.