16 domin sun ƙi su bi ka'idodina da dokokina. Suka ɓata ranar Asabar ɗina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumaka.
17 “Duk da haka na yafe musu, ban hallaka su ba, ban kuma shafe su a jeji ba.
18 Sai na ce wa 'ya'yansu a jeji, ‘Kada ku bi dokokin ubanninku, ko kuwa ku kiyaye ka'idodinsu, kada kuma ku ɓata kanku da gumakansu.
19 Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka'idodina sosai.
20 Ku kiyaye ranar Asabar ɗina domin ta zama alama tsakanina da ku, domin kuma ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’
21 “Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.
22 Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al'umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar.