20 Ku kiyaye ranar Asabar ɗina domin ta zama alama tsakanina da ku, domin kuma ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’
21 “Amma 'ya'yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.
22 Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al'umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar.
23 Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al'umma, da sauran ƙasashe
24 domin ba su kiyaye ka'idodina da dokokina ba, suka ɓata ranar Asabar ɗina, suka bauta wa gumakan kakanninsu.
25 Sai kuma na ba su dokoki da ƙa'idodi marasa amfani, waɗanda ba za su rayu ta wurinsu ba.
26 Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.