22 Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al'umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar.
23 Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al'umma, da sauran ƙasashe
24 domin ba su kiyaye ka'idodina da dokokina ba, suka ɓata ranar Asabar ɗina, suka bauta wa gumakan kakanninsu.
25 Sai kuma na ba su dokoki da ƙa'idodi marasa amfani, waɗanda ba za su rayu ta wurinsu ba.
26 Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.
27 “Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba.
28 Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’