21 Gama Sarkin Babila yana tsaye a mararrabar hanya, inda hanyar ta rabu biyu, yana yin dūbā, yana girgiza kibau, yana neman shawara wurin kan gida, yana dūbān hanta.
22 A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi.
23 Amma a gare su dūbān nan ba gaskiya ba ce, gama sun riga sun yi rantsuwa mai nauyi, amma zai tuna musu da laifinsu, don a kama su.
24 Domin haka ni Ubangiji Allah na ce, tun da yake kun sa a tuna da laifofinku, an kuma tone su, laifofinku kuma sun bayyana cikin ayyukanku, kun tonu, to, za a kama ku a cikinsu.
25 “Kai kuma ƙazantaccen mugu, yariman Isra'ila, ranarka ta zo, lokacin hukuncinka ya yi.
26 Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma.
27 Halaka, halaka, zan hallakar, ba za a bar ko alama ba, sai mai shi ya zo, shi ne zan ba shi.”