9 Akwai mutane a cikinka waɗanda suke haddasa rikici don su zubar da jini, akwai kuma mutanen da suke cin abinci a matsafai, akwai mutanen da suke aikata lalata.
10 A cikinka, mutane suna kwana da matan mahaifansu, waɗansu suna kwana da mata a lokacin hailarsu.
11 Wani yakan yi lalata da matar maƙwabcinsa, wani kuma ya kwana da matar ɗansa, wani ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa.
12 A cikinka mutane suka karɓi toshi don su zub da jini. Kana ba da rance da ruwa da ƙari, kana kuma cin riba a kan maƙwabcinka saboda cutar da kake yi masa, ka kuwa manta da ni, ni Ubangiji na faɗa.
13 “‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar.
14 Zuciyarka za ta iya ɗaurewa, hannuwanka kuma za su ƙarfafa a ranar da zan gamu da kai? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.
15 Zan watsar da kai cikin al'ummai, in warwatsa ka cikin ƙasashe, zan kawo ƙarshen mugayen ayyukanka.