1 Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ɗan mutum, akwai waɗansu mata biyu, uwarsu ɗaya.
3 Sun yi karuwanci a Masar, a lokacin 'yan matancinsu, aka rungumi mamansu da ƙirjinsu.
4 Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
5 Ohola ta yi karuwanci sa'ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa,
6 waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha'awa, suna bisa kan dawakansu.
7 Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.