7 Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta,Ta zubar da shi a kan dutse,Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.
8 Don a tsokani fushina har in yi sakayya,Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse,Don kada a rufe shi.’
9 “Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce,‘Kaitonka, ya birni, mai zubar da jini!Ni kuma zan tsiba itace da yawa.
10 Ka tula gumagumai, ka kunna wuta,Ka tafasa naman sosai,Ka zuba kayan yaji a ciki,Ka bar ƙasusuwan su ƙone.
11 Ka ɗora tukunyar da ba kome cikinta a bisa garwashiDomin ta yi zafi, tagullarta ta yi ja wur,Domin dauɗarta ta narke a ciki,Tsatsarta kuma ta ƙone.
12 Ta gajiyar da ni a banza,Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.
13 Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki.Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba,To, ba za ki ƙara yin tsabta ba,Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’